Dangote ya sasanta da dillalan fetur na Nigeria

0
70

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN ta ce yayan ta sun cimma yarjejeniyar fara sayen man fetur daga matatar man Dangote.

Shugaban kungiyar ta IPMAN na Nigeria Abubakar Garima, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin bayan sun gudanar da wani taro.

Karanta karin wasu labaran:A A Rano, AYM Shafa, da Matrix sun yi karar Dangote, akan hana siyo fetur daga kasashen waje

Ya ce hadin gwiwa da matatar Dangote zai taimaka wajen samun wadataccen man fetur cikin sauki a Nigeria.

Shugaban na IPMAN ya bukaci mambobin su, su mara wa matatar Dangote baya, inda ya ce hakan zai farfaÉ—o da yanayin hada-hadar man fetur da kuma rage karancin sa.

Matatar Dangote ta yi alkawarin fara sayar da man fetur ga mambobin IPMAN sama da 30,000 da kuma gidajen mai 150,000 a fadin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here