A karon farko kowanne Bitcoin daya ya kai dala dubu 80

1
92

A karon farko cikin tarihin kasuwar crypto, a yau lahadi an samu gagarumar nasara inda kowanne Bitcoin daya ya kai dala dubu 80, wanda ba’a taba ganin hakan ba a baya.

Hakan baya rasa nasaba da nasarar Donald Trump, ta lashe zaben shugaban kasar Amurka, zaben 5 ga Nuwamba.

Trump, ya kasance mai goyon bayan harkokin kasuwancin Crypto, yayin da Kamala Harris, da suka yi takara da tare bata goyon bayan harkokin crypto.

Dama anyi hasashen cewa in har Trump, ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, kasuwar crypto zata samu alkairi masu yawa, saboda yayi alkawarin taimakawa crypto, kuma shima daya ne daga cikin manyan yan crypto na duniya.

A yanzu darajar kowanne Bitcoin daya ta doshi naira miliyan 140,000,000.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here