Wata matar aure ta kashe mijin ta da wuka

0
75

Kotu ta aike da wata matar aure zuwa gidan yari kan zargin caka wa mijinta wuka wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mijin har lahira.

Mai Shari’a Olabisi Ogunkanmi ce ta ba da umarnin tsare matar mai shekaru 33 a duniya.

Babbar Kotun Majistire da ke zamanta a Ibadan, ta bayar da umarnin bayan ta yi watsi da ikirarin wadda ake zargin cewa kotun ba ta da hurumin saurar shari’ar.

Daga nan kuma ta daga sauraron zuwa ranar 25 ga watan Maris, na 2025.

An gurfanar da wadda ake zargin ne kan laifin aikata kisa, inda dan sanda mai gabatar da kara Akeem Akinloye, ya bayyana cewa a ranar 30, ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 9 na dare matar ta soka wa mijinta mai shekara 39 wuka, ya mutu.

Jami’in ya shaida wa kotu cewa matar ta halaka mijin nata ne a yayin da suka samu sabani a gidansu da ke garin Ibadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here