Yan ta’adda sun fara yiwa matan aure fyade a Benue

0
75

Al’ummar yankin Ukwonyo dake karamar hukumar Ado, a jihar Benue, sun ankarar da mutane akan yadda yan ta’adda ke cin zarafin mata lokacin da suka je gonaki.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa karuwar irin wannan matsala shine babban abin damuwa, bayan haka kuma an jefa firgici a tsakanin al’umma da suka kauracewa zuwa gonaki don tsoron abun da ka’iya faruwa dasu mara dadi daga yan bindiga.

Sakataren yada labarai na cigaban Ufia, Kwamared Jude Onwe, ya sanar da manema labarai cewa a yanzu haka zuwa debo ruwa ko samo itacen girki ya zama babbar barazana a gare su, inda ya nemi gwamnatin tarayya ta kawo musu daukin jami’an tsaro.

Yace Mata basu da ikon zuwa gonaki ba tare da rakiyar maza ba, saboda suna fuskantar cin zarafi kala kala daga yan bindiga.Ya kafa hujja da cewa wata mata mai shekaru 42, hadi da wasu mata 4 sun tsallake rijiya da baya daga farmakin yan bindigar da suka so yi musu fyade.

Onwe, yace sun sanar da shugaban karamar hukumar Ado abin da ke faruwa wanda ya bayar da umarnin gaggauta bawa matan da aka yiwa fyaden kulawa a asibiti da kuma kokarin neman daukin jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here