Yan ta’adda sun cire kawunan manoma 10 a jihar Niger

0
81

Akalla manoma goma yan ta’adda suka kashe cikin su har da mata a kauyukan Wayan da Belu-Belu, na karamar hukumar Rafi dake jihar Niger.

Al’ummar yankin da abin ya faru sun ce maharan sun yiwa shida daga cikin manoman yankan rago tare da tafiya da kawunan 6 daga cikin mutanen.

Sannan sun ce wasu mutanen da suka tsira da rayuwar su sun ji munanan raunukan harbin bindiga, wanda yanzu haka ake basu kulawa a karamin asibitin Kagara dake karamar hukumar Rafi.

Daily trust, ta rawaito cewa bayan wannan mummunan aiki da yan bindigar suka yi, sun kuma yi garkuwa da mutane da yawa, da asubahin ranar talata lokacin da ake yin Sallar asbah da misalin karfe 5 na dare.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na Niger Bello Abdullahi Muhammad, yace gwamnatin jihar ta samu labarin faruwa lamarin, tare da cewa an bawa jami’an tsaro umarnin hana faruwar hakan a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here