Kananun yaran da gwamnati ta kama sun shaki iskar yanci

0
58

Zuwa yanzu kananun yaran da gwamnatin tarayya ta kama sun dauki hanyar haduwa da iyayen su sakamakon fitar wasu hotuna da suka nuna yaran dauke da wasu jakunkuna, sannan an saka su a mota don mayar da su jihohin su.

A jiya ne dai shugaban Nigeria Tinubu, ya bayar da uarnin sakin yaran bayan sukar da al’umma suka yiwa gwamnatin sa akan kamen kananun yaran da basu zarce shekaru 15 ba.

Karanta karin wasu labaran:Shugaban Nigeria ya nemi a ladabtar da jami’an tsaron da suka kama kananun yara lokacin zanga zanga

Kananun yaran yan arewa sun shafe watanni uku a hannun jamia’an tsaro, ba tare da an gurfanar da su ba, wanda suka galabaita saboda tsananin yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here