Shugaban Nigeria ya nemi a ladabtar da jami’an tsaron da suka kama kananun yara lokacin zanga zanga

0
114

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gaggauta sakin kananun yaran da aka kama a arewacin kasar lokacin zanga zangar neman shugabanci na gari da ta gudana a watan Ogusta.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ne ya sanar da hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa a yau litinin.A cewar Idris, Tinubu, ya bayar da umarnin sakin kananun yaran ba tare da bata lokaci ba, ko kuma jan kafa.

Tinubu, ya kuma bawa ma’aikatar jinkai ta kasa umarnin kulawa da walwalar yaran har a kai su ga iyayen su.An kuma bayar da umarnin kafa wani kwamitin da zai bibiyi yadda aka tafiyar da lamarin kama yaran da yadda aka kula dasu a hannu jami’an tsaro.

Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, ya kuma bayar da umarnin bincikar jami’an tsaron da suka kama yaran.

Idan za’a iya tunawa an gurfanar da kananun yaran a gaban wata Kotun tarayya dake Abuja, da zargin cin amanar kasa, da kuma yunkurin juyin mulki a Nigeria, wanda kotu ta bayar da su beli akan naira miliyan 10 kowanne yaro daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here