Majalisar dinkin duniya tana son magance talaucin Nigeria a shekarar 2030

0
67

Majalisar dinkin Duniya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta taimaka wa Najeriya ta ga bayan talauci da ya yi wa al’ummar ta katutu.

Majalisar ta ce za ta cimma hakan ta hanyar bin tsare tsaren ci gaban muradun Karni nan da zuwa shekara ta 2030 kamar yadda aka tsara.

Bayanin hakan ya fito daga bakin wakilin Jin-ƙai na majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mohamed M. Malick, a lokacin da yake jawabi a Abuja a yayin taron cikar Majalisar Ɗinkin Duniya shekaru 79 da kafuwa.

Ya ce, suna fatan cimma burin su nan da shekara ta 2030 kuma za a ci gaba da bai wa Æ´an Najeriya tallafi a kowane É“angare domin inganta rayuwarsu.

Ministan Matasan Najeriya, Ayodele Olawande wanda ya yi jawabi a madadin Gwamnatin Tarayya, ya ce akwai buƙatar masu ruwa da tsaki su taka mahimmiyar rawa wajen inganta rayuwar matasa don su samu kyakkyawar makoma.

Ministan ya ce, Nijeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da tarin matasa waɗanda kaso kusan 70 ba su haura shekaru 35 ba kuma suna da zimmar kawo sauyi a ɓangarori daban-daban na rayuwa da za su samar da ci-gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here