Kotu ta hana a bawa jihar Rivers kudi daga gwamnatin tarayya

0
69

Mai shari’a Joyce Abdulmalik na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umarci babban bankin kasa CBN da ya dakatar da bawa jihar Rivers kasonta na kudi daga asusun gwamnatin tarayya da ake bawa kowacce jiha a wata wata.

Mai shari’a Abdulmalik ya ce kudaden kason da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yake amsa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya sabawa doka, kuma dole a dakatar ba bashi kudin.

Mai shari’ar ya ce gabatar da kasafin kudin da gwamna Fubara ya yi a gaban yan majalisar jihar guda hudu kawai ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999.

Haka be yasa mai shari’ar ya bukaci babban bankin Najeriya da akanta-janar na kasa da bankin Zenith da bankin Access da su tabbatar Fubara bai ci gaba da amfani da kason jihar na wata-wata ba.

A baya Fubara ya kasance mai samun rashin fahimta tsakanin sa da wasu yan majalisar jihar masu goyon bayan mininstan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, wanda suke bawa Fubara tarnaki wajen gudanar da ayyukan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here