Za’a gina tashoshin lantarki masu amfani da hasken rana a jihohin Arewa

0
77

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta gina manyan tashoshin lantarki masu amfani da hasken rana a kowacce daga cikin jihohin arewacin Nigeria.

Karanta karin wasu labaran:Ministan lantarki ya hana karbar kudin wuta a arewa

Ministan ya ce gwamnatin ta fara tattaunawa da ’yan kwangila kan yiwuwar samar da megawat 100 na wutar lantarki mai amfani da hasken rana a duk jihar da ke yankin, duba da cewa akwai wadatar hasken rana a arewa.

Adebayo ya ce za a gina tashoshin ne da nufin tabbatar da samuwar tsayayyiya kuma wadatacciyar wutar lantarki a fadin yankin.

Ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu kan lalacewar wutar yankin na kimanin kwanaki 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here