Majalisar dattawa ta jingine tantance sabbin ministoci

0
60

Majalisar dattawa ta daga lokacin tantance sabbin ministoci da shugaban Kasa Tinubu ya aike mata da bukatar hakan.

Majalisar a baya ta tsara zata tantance sabbin ministocin a yau lalata.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin majalisar dattawa Sanata Bashir Lado, shine ya sanar da hakan, inda yace anyi hakan don bawa sabbin ministocin da aka tsaba damar shirya takardun da za’a yi amfani da su kafin tantancewar.

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne shugaban kasa Tinubu ya yiwa majalisar zartarwa ta kasa kwaskwarima, inda ya cire wasu daga cikin ministocin sa da Kuma nada wasu sabbi, tare da yiwa wasu ma’aikatun tarayya gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here