Donald Trump ya sha alwashin korar baki daga Amurka

0
62

Dan takarar shugabancin kasar Amurka, na jam’iyyar Republican a zaben wata mai kamawa, Donald Trump ya gudanar da gagarumin taron yakin neman zabe wanda dandazon magoya bayan sa suka halarta a birnin New York.

A cikin jawabin da ya shafe kusan sa’a guda yana yi dan takarar na Republican ya ce zai kawo karshen hauhawar farashi, da kuma tabbatar da tsaron kan iyakokin Amurka.

Karanta karin wasu labaran:Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya je Isra’ila don tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Ya ce, a rana ta farko da zai kama aiki in aka zabe shi zai yi gagarumar korar baki da ba a taba gani ba a Amurka.

 Sannan yace zai kori dukkan wasu masu laifi in har ya samu nasarar zama shugaban Amurka.

Sauran wadanda suka gabatar da jawabi a wajen taron sun hadar da babban tattajirin duniya Elon Musk da matar Trump Melania, wadda ba’a fiya ganin ta a wajen yakin neman zaben Trump ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here