Karancin masu siyan fetur zai sa a rufe gidajen mai dubu 10

0
126
man fetur
man fetur

Sakamakon mummunar tsadar da farashin litar man fetur tayi an samu raguwar mutanen da ke iya siyan man don yin bukata da shi.

Saboda haka dillalan man fetur sun bayyana damuwar su akan babbar asarar da hakan yake kawo musu, wanda ta dalilin haka zasu rufe gidajen mai dubu 10 a fadin Nigeria Wasu alkaluma daga hukumar kula da albarkatun mai na tsandauri da na cikin ruwa, sun nuna cewa adadin man da ake amfani da shi a Nigeria yayi kasa zuwa lita miliyan 4 da dubu dari 5, a kowacce rana a watan Ogusta na wannan shekara, sabanin yadda a kowacce rana ake yin amfani da lita miliyan 60 kowacce rana a watan Mayun shekarar 2023, haka ya nuna cewa an samu raguwar amfani da man da kusan kaso 92 cikin dari.

Haka zalika alkaluman sun ce jihohi 16 cikin 36 na kasar nan ne suka iya samun man fetur daga kamfanin NNPCL a watan Ogusta wanda wannan koma bayan da aka samu na daga cikin dalilin samun karancin man da dogwayen layukan ababen hawa a gidajen man.

Wannan matsalolin sun samo asali tun bayan da shugaban Nigeria Tinubu ya cire tallafin man fetur, da hakan ya mayar da farashin sa ya zarta naira dubu 1 daga naira 175, akan kowacce Lita.

Kungiyar masu gidajen mai ta kasa tace raguwar amfani da man ya sanya mambobin ta asarar da dole se sun rufe fiye da gidajen mai dubu 10, da hakan zai sa ayi asarar ayyukan yi na mutane miliyan 1 a kasar nan.

Mai magana da yawun kungiyar Dr Joseph Obele, yace kudin da ake biyan motar dakon man fetur ya tashi daga naira miliyan 7 zuwa miliyan 47.

Tsadar man dai ta zama wata babbar masifa ga yan Nigeria musamman yadda suka afka cikin kunci da tsadar rayuwa, duk da haka ana cigaba da samun karuwar farashin babu kakkautawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here