Har yanzu ana neman gawar ma’aikatan NNPCL da suka yi hatsarin jirgin sama

0
62

Kamfanin mai na NNPCL ya fitar da sanarwar cewa bayan gawar mutane uku da aka samu har yanzu ba’a kara samun komai ba, bayan da jirgin ma’aikatan kamfanin yayi hatsari ranar alhamis a birnin Fatakwal.

Jirgin ma’aikatan mai saukar ungulu yayi hatsarin a lokacin da ma’aikatan ke yin ziyarar aiki.

Shugaban sashin yada labarai na kamfanin Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yau 27 ga watan Oktoba.

Kamfanin NNPCL yace a halin yanzu ana cigaba da aikin neman ragowar mutanen da ba’a gani ba, ta hanyar hada kai da hukumomin da abin ya shafa.

Olufemi Soneye, yace ma’aikatan NNPCL suna cigaba da yin addu’a ga wadanda abin ya shafa, da kuma taya iyalan su alhinin faruwar mummunan hadarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here