Asusun bayar da lamuni na daniya ya nesanta kansa da cire tallafin man fetur a Nigeria

0
84
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Asusun bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya ce ba shi da hannu a cire tallafin man fetur da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

IMF ya ce Tinubu gaban kansa ya yi wajen cire tallafin man amma asusun bai ba shi shawarar yin hakan ba.

Daraktar IMF a nahiyar Afirka, Abebe Selassie ce ta bayyana hakan lokacin da ta yi hira da manema labarai a birnin Washington na Amurka a ranar Juma’a.

Amman Selassie ta ce cire tallafin man fetur din na daya daga cikin dabarun samar da bunkasa tattalin arziki mai dorewa a Nigeria.

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023 ne Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin bayan rantsar da shi kafin kama aiki.

Tun bayan sanar da cire tallafin man fetur din ne farashin litar mai take hauhawa inda a yanzu ake sayar da man akan kusan N1150 zuwa sama.

Tun kafin yanzu wasu yan Nigeria ke dora alhakin cire tallafin akan bankin duniya da asusun bayar da lamuni na da

duniya, saboda yawan bashin da kasar nan ke ciyowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here