Matatar Dangote ta fara siyar da fetur ga yan kasuwa kai tsaye

0
40

Matatar man fetur ta Dangote ta fara sayar da man fetur kai tsaye ga yan kasuwa bayan janyewar dillancin man da babban kamfanin mai na NNPCL ya yi.

Yan kasuwa da dama wadanda suka jima suna shigo da man daga waje sun kagu a fara sayar musu da man kai tsaye daga matatar ba tare da wani mai dillanci a tsakiya ba.

Karanta karin wasu labarin:Ana shirin kara farashin man fetur a Nigeria

A makonnin da suka gabata ne dai babban kamfanin mai na kasa NNPCL ya sanar da janyewa daga dillancin man na Dangote, domin bai wa ‘yan kasuwa damar sayen man kai tsaye daga matatar. 

Ana ganin wannan matakin zai kawo sauki ga karancin man fetur da ake fuskanta a wasu sassan Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here