Tsohon gwamnan Kano Shekarau yana son kawo karshen siyasar uban gida  

0
115

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya fara jagorantar wata tafiya domin samar da shugabanci na gari a Nijeriya.

Wata tawaga da ya jagoranta zuwa Abeokuta ta ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon ministan tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma, domin neman shawarwari kan kungiyar.

Karanta karin wasu labaran:Ana shirin kara farashin man fetur a Nigeria

A yayin ziyarar, tsohon gwamnan na Kano, ya shaida wa manema labarai cewa babban dalilin da ya sa suka fara tuntubar masu ruwa da tsaki shi ne, nemo wa Nigeria mafita.

Shekarau, ya ce a cikin tafiyar da suka fara suna son su zaburar da al’umma tun daga matakin mazaba har zuwa matakin kasa domin su gano wadanda za su yi musu adalci idan suka ba su shugabanci.

Shekaru yace a yadda ake tafiya an mayar da siyasa ta zama ta kudi, ta zama ta ubangida, suna dora mutane shugabanci ko sun iya, ko ba su iya ba, ko sun dace, ko ba su dace ba, ko suna da kwarewa ko ba su da ita, kuma duk yadda suka dama haka ake sha.

Shekarau, ya ce suna son su zaburar da ‘yan kasa daga Arewa da ke da kuri’a mafi yawa da ma kasa baki daya su daina la’akari da abin da ake ba su ranar zabe ta yadda wasu ke dasa shugabannin da ba su dace ba.

Kazalika, ya ce za su nemi hadin kan duk wanda yake son bayar da gudunmawa kuma za su samu nasara.

Ya ce babbar manufarsu ita ce a samar da shugabanci na gari a Nijeriya.

A ranar Talata ne  tawagar ta mutum 20 ta shugabannin arewacin Najeriya karkashin jagorancin Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka gana da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta.

Tawagar dai ta je gidan tsohon shugaban na Najeriya da manufar lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye arewacin Najeriya da ma faɗin kasa baki ɗaya.

Da farko tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da yadda rarrabuwar kai tsakanin yan kasa ya jawo wa Nigeria koma baya.

Sai dai Obasanjo ya ce duk da wadannan matsaloli da ake ke fuskanta har yanzu yana da kyakkyawan fata a kan Najeriya.

Obasanjo ya bayyanawa tawagar cewa kun ayyana kanku a matsayin kungiyar masu son dimokradiyya ta arewacin Najeriya, amma na so a ce kun kira kanku kungiyar cigaban dimokradiyya ta Najeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here