Nigeria ta hana fitar da Gas din girki zuwa kasashen waje

0
78

Gwamnatin tarayya ta hana fitar da gas din girki zuwa kasashen waje, daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa, a wani mataki don hana hauhawara farashin gas din.

Karamin ministan albarkatun mai kula da harkokin gas, Ekperikpe Ekpo, ne ya bayyana haka, a cikin irin matakan da ya ce gwamnati ta dauka domin tabbatar da saukin gas wanda yake kan yin tsada.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnati ta dena karbar haraji akan Gas din girki

Ministan ya ce akwai damuwa kan yadda farashin gas ke ta hauhawa tsakanin naira 1,100 da 1,250 zuwa naira 1,500 a kan kowanne kilo daya.

A kan hakan ministan ya yi taro da masu ruwa da tsaki a kan gas a Abuja ranar Talata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, domin lalubo hanyoyin magance matsalar hauhawara farashin.

A nan ne ministan ya sanar da cewa daga cikin muhimman matakan da aka dauka akwai umartar kamfanin mai na NNPCL da masu samar da gas a cikin kasa da su daina fitar da gas din da aka samar a Nigeria zuwa waje.

Ekpo ya jaddada bukatar ganin an samar da tsayayyen tsari na tsayar da farashin gas wanda zai dace da bukatar yan Nigeria.

A wata sanarwa da kakakin ministan, Louis Ibah, ya fitar ya ce an bai wa hukumomin da ke aikin hakowa da sayar da albarkatun mai na kasar umarnin su fitar da wani tsarin farashin gas na cikin gida nan da kawana 90.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here