Majalisar dokokin Kano tace babu abinda za’a hana zaben kananun hukumomi

0
99

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar cewa za’a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024, duk da hukuncin Kotun Tarayya na hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) gudanar da zaben. 

Kotu ta bayar da umarnin sauke shugabannin KANSIEC da wasu mambobin ta saboda alakar su da siyasar jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano, amma gwamnatin jihar ta jaddada kudurinta na ci gaba da gudanar da shirin zaben, ko da babu jami’an tsaro.

Karanta karin wasu labaran:Kotun tarayya ta rushe shugabannin hukumar zaben Kano KANSIEC

Lawal Hussain Dala, Shugaban Masu Rinjaye, na majalisar dokokin Kano, ya soki hukuncin kotun, inda ya bayyana cewa ya saba da umarnin da Alkalin wata  Kotu Mai Shari’a Nura Ma’aji ya bayar, wanda ya hana jam’iyyun siyasa tsoma baki a harkar zaben.

Lawal, yace umarnin Kotun Koli ya bukaci jihohi su gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen watan Oktoba.

KANSIEC ta fuskanci kalubale saboda tsadar kudin fom din takara, kan Naira miliyan 10 ga dan takarar shugabancin karamar hukuma da miliyan biyar na kansila.

Amma daga bisani ta rage bayan shigar da kara a Kotun Tarayya.

Har ila yau, wata Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarni na hana jam’iyyun siyasa tsoma baki a shirin zaben, wanda ya bai wa KANSIEC damar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here