An samu muggan kwayoyi a gidan wani Sanata

0
73

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta samu nasarar gano muggan kwayoyi masu bugarwa a gidan Sanata Oyelola Yisa Ashiru, na jam’iyyar APC, mai wakiltar kudancin jihar Kwara.

Shugaban hukumar Burgediya Janar Muhammad Buba Marwa, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake jawabi ga manema labarai.

Yace jami’an hukumar NDLEA ne suka mamaye gidan Sanatan dake birnin Ilorin tare da binciko kwayoyin.

Karanta karin wasu labaran:NDLEA ta kama yar kasar Canada da muggan kwayoyi

Mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ne ya sanar da hakan a yayin gabatar da jawabin a madadin Buba Marwa, inda yace an kama masu taimakawa Sanatan su uku sannan aka gurfanar da su har an yankewa daya hukuncin zaman gidan gyaran hali a watan Yuni na wannan shekara.

Babafemi, ya kalubalanci kalaman Sanata Oyelola, da ya ayyana hukumar NDLEA da cewa tana aiwatar da cin hanci da rashawa a ayyukan ta.

A kwanakin baya jaridar Daily Trust, ta rawaito labarin da Sanata Oyelola, yake cewa hukumar NDLEA ce babbar hukumar gwamnati mai aiwatar da cin hanci da rashawa a fadin Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here