Kudin yan fanshon Nigeria ya kai naira triliyan 21

0
75

Kadarorin fansho a kasar nan, sun karu zuwa Naira biliyan 345, wanda hakan ya nuna cewa, a watan Agustan 2024, sun kai Naira tiriliyan 21.

Kudaden adashin gata na kadarorin fanshon, a karshen watan Agustan 2024, sun kai Naira tiriliyan 21.14, sabanin Naira tirilyan 20.79, da aka samu a watan Yulin 2024, wanda hakan ya nuna cewa, sun karu da Naira biliyan 345.65.

Karanta karin wasu labaran:Bayanin yadda zaka yi nasara a mining din Memefi lokacin listing

Bisa bayanan da aka fitar na baya- bayan nan, daga hukumar kula da fansho ta kasa (PenCom), sun nuna cewa yawan ma’aikatan da suka yi ritaya sannan suka zuba kudadensu na yin ritaya a cikin asusun ajiya na masu ritaya wato (RSA), sun karu zuwa 10, 457,073 a karshen watan Augustan 2024, daga 10,419,520 da aka samu a watan Yuli.

Sai dai gwamnatin kasar nan ta ci gaba da cin bashi daga asusun ajiya na ‘yan fansho da suka yi ritaya daga ma’aikatan gwamnati.

Adadin kudin da gwamnatin ke zubawa, sun kai yawan Naira tiriliyan 13.40, a watan Agusta, wanda kuma kudin da gwamnatin ta zuba suka kai yawan Naira tirilyan 12.59, inda kuma sauran Naira tirilyan 2,04, ke bi a baya, sai kuma shiya din cikin gida da suka kai Naira tirilayan 1.94.

Haka zalika bisa bayanan da aka samu daga PenCom, a zango na biyu na 2024, mutane sun zuba kudadensu a cikin asusun RSA da ya kai Naira biliyan 377, wanda kuma daga bangaren gwamnati, aka zuba Naira bilyan 217, sai kuma a bangaren masu zaman kansu, suka zuba Naira bilyan 160.83.

A zango na biyu na 2020, bangaren gwamnati ta zuba Naira biliyan 118.50, inda kuma na masu zaman kansu, aka zuba kasa da Naira biliyan 70.69.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here