Za’a binciki dalilin fashewar tankar man da ta kashe mutane a Jigawa

0
116

Hukumar gudanar da bincike akan hadarurruka da lafiyar al’umma ta kasa zata gudanar da babban binciken dalilin faruwar tashin gobarar tankar man da tayi sanadiyyar rasuwar mutane 157 a Karamar hukumar Majiya dake jihar Jigawa

Mahukuntan jihar sun ce kawo yau alhamis adadin mutane 157, aka tabbatar gobarar motar dakon man tayi sanadin mutuwa, sai kuma karin mutanen dake kwance a asibiti suna jinya.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Jigawa zata fara samar da wutar lantarki

Daraktar yada labarai ta, hukumar gudanar da binciken, Bimbo Olawumi Oladeji, ce ta sanar da hakan, inda tace hukumar ta san masifar dake tattare da fashewar tankar mai.

Lamarin ya faru da misalin karfe 11 na daren talata lokacin da motar dakon man data taso daga Kano zuwa Yobe ta kufcewa direban ta hakan yasa motar ta kife.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin wadanda iftila’in ya shafa sun rasu Sakamakon dibar man fetur daga motar data fadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here