Har yanzu babu lokacin siyarwa yan kasuwa fetur daga matatar Dangote

0
75

Za’a iya cewa har yanzu tsugune bata kare ba dangane da batun siyarwa yan kasuwa man fetur kai tsaye daga matatar Dangote, yayin da har yanzu matatar kamfanin NNPCL kadai take siyarwa man ba tare da siyarwa yan kasuwa ba kamar yadda gwamnatin tarayya tace ta bada dama.

Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin NNPCL da Kungiyar kungiyar dillalan man fetur IPMAN

Dillalan man fetur din a ranar laraba sun ce kamfanin NNPCL zai cigaba da zama mai siyo man daga Matatar Dangote su Kuma suna siya a hannun NNPCL har sai an kawo karshen lokacin yarjejeniyar siyan fetur din dake tsakanin NNPCL da Dangote.

Sai dai yan kasuwar basu bayyana lokacin da za’a kawo karshen yarjejeniyar kasuwancin a tsakanin NNPCL da matatar man fetur ta Dangote ba, haka zalika suma wakilan NNPCL da na Dangote sun ki cewa komai akan kawo karshen siyarwa da NNPCL man.

A ranar 11 ga watan Oktoba ne wata sanarwa daga ma’aikatar kudi ta Nigeria tace dillalan man fetur yan kasuwa suna da damar siyo man kai tsaye daga matatar Dangote, amma da alama hakan yana neman gagara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here