Dattawan arewa sun ce shugaba Tinubu yana Kokarin magance rashin tsaro a yankin

0
70

Kungiyar dattawan Arewa ta yabawa kokarin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yaki da rashin tsaro a yankin.

Shugaban kungiyar dattawan Arewa reshen Arewa maso Yamma, Alhaji Mustafa Aliyu Dutsin Ma, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya yaba da sabuwar dabarar da Tinubu ya bullo da ita wanda aka yi wa lakabi da “Fansan Yamma,” inda yace hakan ya samar da sakamako mai kyau a yaki da rashin zaman lafiya a arewa.

A cewar dattawan Arewa, yadda shugaba Tinubu ya yi kaurin suna wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman matakin da ya dauka na yin amfani da karfin soji wajen murkushe ‘yan bindiga a maboyarsu ba tare da daga kafa ba, hakan ya haifar da samun nasarar yaki da rashin tsaro.

Karanta karin wasu labaran:Majalisa ta nemi Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025

Kungiyar ta bayyana kwarin gwiwa kan yadda Tinubu yake tunkarar lamarin rashin tsaron.

A kwanakin baya ne karamin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle ya kai ziyara yankin gabashin jihar Sokoto, inda ayyukan ‘yan fashi suka ta’azzara.

Dattawan Arewa sun bayyana wannan ziyarar a matsayin “babbar nasara” a yakin yakin da Shugaba Tinubu ke yi da rashin tsaro.

Mun gamsu da matukar farin ciki cewa gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Tinubu a shirye take ta tunkari matsalar rashin tsaro da kakkausar murya, tare da kokarin ruguza matsugunin ‘yan ta’adda, inji Kungiyar.

Sai dai a wasu yankunan arewa musamman Zamfara ana cigaba da samun ayyukan ta’addanci, musamman garkuwa da mutane da kashe su babu dalili.

Haka zalika a jihar Sokoto ma ana samun karuwar ayyukan ta’addancin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here