Asibitin Aminu Kano ya kula da wadanda suka kone a Jigawa ba tare da kudin magani ba

0
102

Wasu daga cikin wadanda suka kone a gobarar fashewar tankar man fetur a jihar Jigawa dake karbar magani a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake jihar Kano, sun bayyana tashin hankalin da suka shiga.

Jaridar Daily News 24, ta rawaito cewa an samu fashewar tankar man fetur din a karamar hukumar Majiya dake jihar Jigawa da misalin karfe 11 na daren talata.

Zuwa yammacin yau talata an tabbatar da mutuwar mutane 157, sannan adadin da ba’a kammala tantancewa ba suna cigaba da karbar magani a gida da asibiti.

 Daya daga cikin wadanda suka tsira da rayuwar su a iftila’in mai suna Yahuza Khamisu, ya bayyana wa Daily News 24, cewa da misalin karfe 11 na daren talata suka samu labarin faduwar tankar man lokacin da suke hutawa a gida, bayan samun labarin ne al’umma manya da yara suka fito domin yin kallo, yayin da wasu ke kwasar man fetur din daya zube, ana tsaka da hakan ne wuta ta tashi, tare da kone mutanen kusa da nesa.

Karanta karin wasu labaran:Za’a binciki dalilin fashewar tankar man da ta kashe mutane a Jigawa

Yace akwai kananun yaran sa 4 da har yanzu ba’a san inda suka shiga ba.

Haka zalika Shima wani da hatsarin ya rutsa dashi mai suna Kabiru Ahmadu, yace lokacin da suka fara jiyo ihun masu neman temako sun yi zaton cewa yan fashi ne suka zo garin, daga nan ne shima ya nemi yayan sa ya rasa, bayan haka kuma aka jiyo fashewar tankar man baki daya.

Shima Muhammad Shu’aibu, wanda tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa ne ya rasa dan sa guda daya, sannan daya ya samu raunika yana karbar magani a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Shu’aibu, ya nemi gwamnati ta rika daukar matakan hana mutane zuwa wajen da irin wannan iftila’i ke faruwa, ta hanyar yin amfani da jami’an tsaro, inda yace hakan zai rage yawan asarar rayuka.

A nasa jawabin Shugaban asibitin koyarwa na Malam Aminu Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, yace sun karbi mutane 32, daga cikin wadanda suka kone, sannan ana basu kulawar data dace, kuma an fara samun nasarar ceto rayuwar su.

Yace kawo yanzu ba’a samu wanda ya rasu a asibitin ba, bayan fara karbar magani.

Yace zuwa yanzu basu nemi ko kwandala daga wajen marasa lafiyar ba, wanda hakan dole ne a ka’idar da gwamnati ta tanada na kula da masu neman daukin gaggawa.

Amman yace zasu kula da marasa lafiyar ne tsawon awanni 48, daga nan dole zasu fara biyan kudaden magani da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here