Gwamnatin Kano zata gyara wajen da aka lalata lokacin zanga zanga

0
78
Zanga-Zanga
Zanga-Zanga

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirin da take yi na gyara wajen koyar da Ilimin na’ura mai kwakwalwa na Digital Industrial Park, dake kan titin zuwa gidan gwamnati, da aka kone tare da kwashe kayayyakin da aka zuba a wajen lokacin zanga zangar neman shugabanci na gari a watan Ogusta.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya bayyana hakan a jiya litinin lokacin da ministan sadarwa Dr Bosum Tijjani, ya ziyarci wajen.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Kano ya sasanta rikicin Baffa Bichi 

Gwarzo, yayi ala wadai da lalata wajen koyar da Ilimin na kwamfutar, yana mai cewa hakan ya mayar da jihar Kano baya a fannin habbaka ilimin zamani na na’ura mai kwakwalwa da kimiyya.

Ma’aikatar sadarwa ta kasa ce ta samar da wajen a zamanin mulkin tsohon shugaban Nigeria Buhari.

Mataimakin gwamnan yace bayan fashe wajen da bata gari suka yi, jami’an tsaro da sauran al’umma masu son cigaba sun yi kokarin karbo wasu daga cikin muhimman kayyakin da mutane suka sace.

Gwamnatin Kano ta bawa ma’aikatar ayyuka ta jihar umarnin yin nazari akan asarar da akayi da kuma shirya fara gyaran wajen cikin gaggawa.

Idan za’a iya tunawa a lokacin zanga zangar neman shugabanci na gari a watan Ogusta an samu rikidewar zanga zangar zuwa tarzoma da sace dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here