Yan wasan Nigeria sun yi barazanar kin buga wasa da Libya  

0
191

Tawogar kwallon kafar gida Nigeria, wato Super Eagles, ta yi barazanar kin shiga wasan neman gurbi a gasar cin kofin Afirka da kasar Libya sakamakon kyale su da akayi a filin jirgin sama na Al Abraq sama da sa’o’i 12 ba tare da sanin mafita ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, hukumar kwallon kafa ta kasa ,NFF ta ce tawagar kasar nan da za ta buga wasan da Libya, har yanzu suna nan a filin tashi da saukar jiragen sama na Al Abrak cikin mawuyacin hali.

Karanta karin wasu labaran:Nigeria zata shiga matsanancin rashin fetur—–IPMAN

Bayan da Libya ta yi rashin nasara a hannun Nigeria da ci 1-0 a ranar Juma’a a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom, ana sa ran kungiyoyin biyu za su sake haduwa a wasan su na hudu cikin rukunin D.

A ranar Lahadi da yamma ne ‘yan wasan na Super Eagles suka tashi zuwa kasar Libya, sai dai kamar yadda rahotanni suka nuna, sa’a daya da sauka a birnin Benghazi, inda jirgin nasu ya nufa, sai aka karkata jirgin na Nigeria zuwa birnin Al Abraq, wani gari mai nisan tafiyar sama da sa’o’i biyu daga Benghazi.

Karkatar da jirgin ne ya kawo dalilin tawagar ta Super Eagles su ka shiga halin rashin tabbas inda su ke makale a filin jirgin saman na Al Abraq ba tare da wani taimako daga hukumar kwallon kafa ta Libya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here