Hisbah ta musluntar da macen da tazo Kano yawon banza

0
101

Rundunar Hisbah ta samu nasarar musluntar da wata yar Jihar Adamawa mai suna maryam wadda tazo jihar Kano domin yawon ta zubar.

Mukaddashin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden ne ya sanar da, inda yace Maryam ta karbi addinin muslinci bayan ta fahimci muhimmancin addinin.

Dr Mujahiddin, ya yabawa Maryam, inda yace burin rundunar Hisbah bai wuce gyara al’umma zuwa hanya mai kyau ba.

Hisbah ta kuma dauki matakin cigaba da dakile mummunar dabi’ar yin caca tsakanin matasan jihar.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta kama matasa maza da mata masu yawon dare

Dr Mujahiddin yace jami’an rundunar su sun kama masu yin caca a kofar Ruwa da Dakata, inda aka kama mutane 19, cikin su har da dattawa masu Shekaru kusan 80, suna yin cacar.

Dr Mujahiddin, yace sun kuma kama wasu mata da ake zargin ana yin lalata da su a unguwar Nassarawa su biyar.

Rundunar Hisbah ta roki al’umma su zama masu yin biyayya ga dokokin Ubangiji don kaucewa afkuwa cikin fushin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here