Yan bindiga sun kashe hakimi bayan garkuwa da shi a jihar Kebbi

0
112

An tabbatar da labarin rasuwar hakimin Kanya a yankin Danko Wasagu, dake jihar Kebbi, Alhaji Isah Daya, bayan yan bindiga sun yi garkuwa da shi a daren ranar lahadi data gabata.

A lokacin garkuwar an kama shi da karin wasu mutane 8 dake garin na kanya.

Duk kokarin da jami’an tsaro sukai na kubutar dashi sun iya yin su, sai dai masu garkuwar sun ji masa mummunan rauni a kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar tasa.

Usman Zaga, daya daga cikin manyan jami’an bagaren tsaro a Kebbi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace jami’an tsaro sunyi musayar wuta da yan ta’addan, har aka samu nasarar ceto mutane 8 da aka sace tare da hakimin.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Kebbi tace za’a iya fuskantar karancin abinci a jihar

Wadanda aka ceto sun hadar da Almustapha Almu, Hajara S. Maikano, Rukayya Isah Daya, Bello Isa Daya, Fa’iza Maikano, Amina Maikano, da Jidah Babangida.

Jami’an hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar SP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da labarin rasuwar hakimin.

Abubakar, yace yan ta’addan sun fafata da jami’an tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda, da yan Bijilanti a dajin Sakaba, inda a nan suka boye wadanda suka yi garkuwar dasu.

Yace babban abin takaici shine an tarar da gawar hakimin lokacin da Jami’an tsaro suke tsaka da aikin ceto mutanen da aka yi garkuwar dasu.

Sannan wadanda aka kubutar su 8 tuni aka hada su da iyalan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here