Cutuka masu yaduwa sun mamaye Kano Jigawa, Lagos da Oyo.

0
119

Jihohin Legas, Jigawa, Kano da Oyo da karin wasu 8 sune ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutuka masu yaduwa musamman cutar amai da gudawa, daga farkon Wannan shekara zuwa yau.

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC, tace akalla mutane 10,837 ake zaton sun kamu da cutar sai 359, da suka mutu bayan kamuwa da cutar amai da gudawa.

Rahotanni daga NCDC sun nuna yadda jihohi 21 suka samu kansu a yanayin barkewar cutar ta Cholera.

Karanta karin wasu labaran:An samu bullar bakuwar cuta a Sokoto – NCDC

Jihohi 9 da masu cutar suka fi yawa sun hadar da  Lagos mai mutane (134), Jigawa (52), Kano (46), Oyo (26), Ebonyi (16), Adamawa (16), Rivers (13), Katsina (12) da kuma Bauchi mai mutane (10).

NCDC ta kara da cewa idan aka kwatanta da shekarar 2023, an samu karin kaso 239, cikin 100, na yawan mutanen da cutar amai da gudawa ta kashe, sannan adadin kaso 220 cikin 100 ya karu akan masu kamuwa da cutar a shekarar data gabata.

Daga cikin abubuwan da ake dora alhakin sun taimaka wajen karuwar cutar akwai ambaliyar ruwa, rashin tsaftace kayan da za’a ci, sai matsalar yin kashi akan hanya.

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC, tace tana yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da hana cutar yaduwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here