Rikici ya kunno tsakanin Rasha da Ukraine akan Nigeria

0
94

Cacar baka ta barke tsakanin mahukuntan kasar Rasha da Ukraine, inda kowanne yake zargin dan uwansa da taka rawa a al’amuran Nigeria na cikin gida.

 Zanga zangar da aka yi a watan Ogusta itace sanadiyyar samun rashin fahimtar tsakanin kasashen biyu.

Karanta karin wasu labaran:Masu zanga zanga sun hadu da fushin jami’an tsaron Abuja

Idan za’a iya tunawa a lokacin da wasu matasan kasar nan suka gudanar da zanga zangar neman shugabanci na gari a kasar nan wadda ta rikide zuwa tarzoma, wasu daga cikin masu zanga zangar sun riga daga tutar kasar Rasha da sunan neman kasar ta Rasha ta shigo Nigeria da dakarun sojin ta, lamarin daya kawo fargaba ga wasu mahukuntan Nigeria, musamman in aka yi nazari akan yadda Rasha ke samun karfi a wasu kasashen Afrika.

Amman a jiya juma’a kasar ta Rasha tayi kakkausan gargadi ga kasashen Amurka, Burtaniya, da Ukraine, wanda suka zargi Rasha da daukar nauyin gudanar da waccan zanga zangar.

Rasha, tace wadannan kasashe su ya kamata a zarga da yiwa al’amuran Nigeria na cikin gida kutse, da Kuma kokarin lalata alakar Rasha da Nigeria.

Gargadin yazo a daidai lokacin da ake yada jita jitar cewa wasu kasashen ketare ne suka dauki nauyin sabuwar zanga zangar da aka yi a Kasar nan ranar 1 ga watan Oktoba.

A lokacin da aka samu Zanga zangar watan Ogusta an samu damar kama masu dinka tutar kasar Rasha a jihar Kano da sauran masu daga tutar.

Tun a Zanga zangar farko jakadan Rasha a Nigeria ya fito bainar jama’a in ya ce ko kadan kasar sa bata da hannu a faruwar lamarin.

Idan za’a tuna tun kafin yanzu ana gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, inda kasashen Turai ke goyon bayan Ukraine tare da bata makamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here