Hisbah ta kama kayan mayen da ake yin safarar su Zuwa Adamawa

0
75
Hisbah
Hisbah

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu muggan kwayoyi masu bugarwa da ake yin safarar su daga Jihar Legas a turo su Kano zuwa jihar Adamawa.

Mukaddashin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa wani da ba’a san shi ba shine yake turo kayan an canja musu kama a cikin kayan sakawa na jaririai, daga Legas zuwa Kano sannan a saka su a mota zuwa Adamawa.

Karanta karin wasu labaran:Rundunar Hisbah ta hana zancen dare tsakanin masoya a Kano

Wanda ake turowa kayan daga Legas shine ya tona asirin masu lefin, sakamakon cewa tun da farko bai san abun da yake kunshe a kayan da ake turo masa don aikewa dasu zuwa Adamawa ba.

Zuwa yanzu hukumar Hisbah tace ta na kan binciko wanda yake turo kayan daga Legas, don hukunta shi.

A kan haka ne hukumar take jan kunnen mutane su rika kula da irin kayan da wasu ke turo musu daga gurare daban daban don kaucewa afkuwa cikin matsala musamman a yanzu da ake cikin kalubalen rashin tsaro.

A wani cigaban, Mukaddashin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, yace a unguwar Panshekara sun samu nasarar bankado wani gidan na babban mutum da yake lalata kananun yara tare da abokan sa.

Hukumar Hisbah, ta kara da cewa sun kama mai gidan da ake lalata da yaran tare da abokan sa masu irin wannan hali, har ma da yan matan da ake lalatawa, kuma za’a yi musu hukunci dai dai da lefin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here