Gwamnati ta dena karbar haraji akan Gas din girki

0
93

Gwamnatin tarayya ta sanar da yin sassaucin haraji akan wasu abubuwan da suka shafi man Diesel da iskar Gas don samar da kyakyawan yanayin kasuwacin fannin.

Gwamnatin tace daga yanzu ta jingine batun karbar harajin siyan kayayyaki wanda aka fi sani da VAT akan Gas din girki da wanda ake yin amfani da shi a abubuwan hawa.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin tarayya zata karawa yan Najeriya haraji

Ministan kudi Wale Edun, ne ya fitar da sanarwar hakan a jiya laraba.

Ministan ya fitar da sanarwar ta hannun shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Muhammad Manga, inda yace hakan zai taimakawa Nigeria wajen cimma manufar habbaka samar da iskar Gas, da mamashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here