Wani mutum zai hallaka kansa saboda mulkin shugaba Tinubu

0
79

Jami’an Yan sanda sun kama wani dan jihar Adamawa da ya hau kan babban turken wutar lantarki sannan yace ba zai sauka ba har sai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya sauka daga shugabancin Nigeria.

Turken wutar lantarkin da mutumin ya hau a Adamawa ya kai girman 33KV, a karamar hukumar Mayo Belwa.

Jami’an Yan sanda sun ce mutumin ya cigaba da kasancewa akan turken wutar lantarkin tare da cewa dole shugaban kasa Tinubu, ya sauka daga shugabancin Nigeria kafin ya sauko.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin tarayya zata hana kungiyar ASUU shiga yajin aiki

Ya zauna akan turken wutar lantarkin tun safiyar juma’a har zuwa yammacin ranar asabar data gabata.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa SP Suleiman Nguruje, yace sun tseratar da mutumin wanda ba’a bayyana sunan sa ba cikin kwanciyar hankali a daren asabar, kuma ana cigaba da tsare shi a hannun yan sandan.

Rundunar yan sandan jihar tace zata gurfanar da shi a gaban kotu da tuhumar yunkurin kashe kansa, kuma hakan babban laifi ne a kundin tsarin mulkin kasa.

A cewar SP Suleiman Nguruje, yan sandan suna da alhakin kare rayuka da dukiyar al’umma, kuma duk wanda yayi yunkurin kashe kansa zai fuskanci fushin hukuma.

A wasu lokutan dai ana samun masu yunkurin kashe kansu a kasar nan, inda wani lokacin masu Wannan yunkuri ke kafa hujja da cewa kuncin rayuwa ne yasa zasu kashe kansu.

ADAMAWA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here