Bankin duniya zai bawa Nigeria tallafin kusan dala biliyan 2

0
103
World Bank on glass building. Mirrored sky and city modern facade. Global capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Bankin duniya mai babban ofishi a birnin Washington na kasar Amurka, zai bawa Nigeria bashin kudin da ya kai dala biliyan 1 da miliyan 57.

Bankin yace za’a yi amfani da bashin don taimakawa gwamnatin tarayya ta inganta cigaban lafiyar yan Nigeria musamman mata da kananun yara masu tasowa.

 Sannan yace za’a saka wani kaso na kudin a fannin dakile mummunan tasirin sauyin yanayi, irin su ambaliyar ruwa, da gyara tafkuna don yin noman rani.

Karanta karin wasu labaran:Yawan bashin da ake bin Nigeria ya zarce Dala biliyan 88

A yau litinin ne bankin ya amincewa Nigeria karbar sabon bashin da za’a yi manyan ayyukan cigaban kasa dasu kuma yawan kudin ya kai dala biliyan 1 da miliyan 57.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ofishin kula da basukan da ake bin Nigeria ya fitar da sanarwar cewa zuwa watan Maris na shekarar da muke ciki ana bin kasar nan bashin da yakai dala biliyan 88.

Masana tattalin arziki na alakanta yawan bashin da Nigeria ke ciyo wa da yanayin tabarbarewar tattalin arziki, kamar tsadar rayuwa da karyewar darajar naira.

WORLD BANK

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here