An rantsar da sabuwar babbar mai shari’a ta kasa

0
91

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya rantsar da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, a matsayin sabuwar babbar mai shari’a ta kasa.

Shugaban ya rantsar da ita yau litinin a zauren majalisar zartarwa dake fadar shugaban kasa a birnin tarayya Abuja.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta dage sauraron shariar wadanda ake zargi da kashe Sheik Aisami

A makon daya gabata ne majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da Kekere-Ekun a matsayin babbar mai shari’ar.

Tun da farko shugaban kasar shine ya nada Kekere-Ekun a matsayin mai rikon mukamin babban mai shari’a na kasa, bayan kammala aiki tsohon babban mai shari’a na na Olukoyede Ariwoola.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here