Hisbah ta kama matar da ke bayar da hayar dakin ta ana lalata mata

0
127
Hisbah
Hisbah

A cigaba da kokarin Hukumar Hisbah na tsaftace Jihar Kano daga aikata badala, hukumar ta kai samame unguwar Titin Filin Sakuwa wanda aka fi sani da titin Race Course, inda ta samu nasarar kama wasu ‘yan mata da ake zargin ana kai su wajen shakatawa ana yin lalata da su.

Daga cikin matan da aka kama an samu mai ciki da kuma mai dauke da jariri.

Karanta karin wasu labaran:Za’a tuhumi ministan tsaro akan zargin alakar sa da yan bindiga

Haka kuma, an kama wata mata da ta mayar da gidanta mafakar badala, tana bayar da haya ga matan don aikata alfasha.

Hukumar tace gidan da ke unguwar Samegu ya zama tamkar dandalin karuwanci.

Hisbah ta kama maza uku da mata uku a lokacin samamen, yayin da ake cigaba da bincike don gano wadanda suka bawa matar hayar gidan da take lalata tarbiyyar al’umma.

Mukaddashin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya tabbatar da hakan labari, yana mai cewa za a dauki tsauraran matakai kan duk wanda aka samu da hannu wajen aikata irin wadannan laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here