A Nigeria ne kadai yan siyasa ke yin sata su zauna lafiya—-NDUME

0
69

Sanata Ali Muhammad Ndume, dake wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa ya bayyana matukar damuwar sa akan tsananin matakin da cin hanci da rashawa ya kai a Nigeria.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yace Ndume ya nuna takaicin nasa a yau lahadi lokacin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Kano.

Karanta karin wasu labaran:Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a Neja da Borno

Yace cin hanci da rashawa ya zama wata babbar annoba a Nigeria saboda a cewar sa yan siyasa suna satar kudaden al’umma kuma suna yin alfahari da yin hakan sakamakon ba’a daukar matakan hana su yin hakan.

Dan majalisar yace rashawa ita ce babbar masifar da Nigeria ke ciki, Kuma ba’a samun sauki kullum abin gaba yake yi, kuma ba’a daukar matakan dakile mummunar al’adar.

Yace babu dan siyasar da baya satar kudaden al’umma ko cin hanci sai dai wanda Allah ya kiyaye, sannan a Nigeria ne kadai mutum zai yi sata Kuma yayi yawon sa zuwa inda yake so babu mai taka masa birki.

Ndume, yace a Nigeria ne kadai zaka ga mutum a yau bashi da ko sisi amma a cikin kwana daya zai sayi motoci 10, da jirage, sannan yan uwansa su je duk inda suke so har iyayen sa su rika cewa Allah ya yiwa dan su albarka.

Sanata Ali Muhammad Ndume, yace tun a baya ya yi kokarin kawo kudirin kafa dokar binciken mutanen da ke samun kudi ba tare da an san hanyar da suka mallaki kudin ba, amma bai samu goyon bayan samar da dokar ba.

Daga karshe ya bayyana damuwar sa akan yadda yunwa ta zama karfen kafa ga yan Nigeria, sannan ya roki a bawa noma muhimmanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here