Za’a tuhumi ministan tsaro akan zargin alakar sa da yan bindiga

0
82

Wata kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta umarci gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike akan zargin karamin ministan tsaro Bello Matawalle, yana da alaka tsakanin sa da yan fashin dajin da suka addabi mahaifiyar sa Zamfara.

Kotun ta bayar da umarnin a matsayin amincewa bukatar da masu karar Matawalle suka suka shigar gaban ta.

Karanta karin wasu labaran:Dole a kawo karshen rashin tsaro a arewacin Nigeria–ACF

Mutanen da aka hada wajen shigar da karar sun hadar da shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, ministan shari’a da babban sufeton yan sanda.

Wani mai rajin kare hakkin bil adama Abubakar Dahiru, ne ya shigar da karar zargin.

Mai shigar da karar ta hannun lauyan sa Ojonimi Apeh, ya roki kotu ta sanya shugaban kasa Tinubu, ya bawa shugaban yan sanda umarnin gudanar da bincike akan ayyukan ta’addanci da fashin daji a Zamfara, musamman zargin da suke yi na cewa tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro Bello Matawalle, yana da cikakkiyar alaka tsakanin sa da yan fashin dajin akan garkuwa da mutane, da kashe kashe.

Mai shigar da karar yace sun yi haka ne don samar da tsaron rayukan al’ummar Zamfara.

Ayyukan rashin tsaro dai sun yi katutu a jihar Zamfara, yayin da yan fashin daji ke cin Karen su babu babbaka, wajen sace mutane da kashe su, tare da sace dabbobi da kashe manom.

Ko a kwanakin da suka gabata sai da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare, yayi wata zantawa da tashar talbijin ta TVC, sannan kai tsaye ya danganta Bello Matawalle, da aikin yan ta’adda.

Sai dai karamin ministan ya musanta zargin da aka yi masa na hada baki da yan fashin daji don su cutar da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here