A karon farko an gudanar da zaben kananun hukumomi a Anambra

0
85

A karon farko an gudanar da zaben kananun hukumomi a jihar Anambra, bayan shafe shekaru 11 ba tare da zababbun shugabannin kananun hukumomin ba.

Yau asabar itace ranar da masu rijistar kada kuri’a suka fita runfunan zabe don zabar shugabannin kananun hukumomi da Kansiloli.

Zaben kananun hukumomi na karshe da aka gudanar a jihar Anambra, an yi shi tun shekarar 2013, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Peter Obi.

Karanta karin wasu labaran:Kotu tayi watsi da bukatar APC akan zaben kananun hukumomin Kano

Tun daga Wancan lokaci ba’a Kuma yin zaben ba, inda magajin Peter Obi, Willie Obiano, ya kammala mulkin sa ba tare da zababbun shugabannin kananun hukumomi ba, sai dai masu rikon kwarya.

Haka zalika shima gwamnan jihar mai ci a yanzu Charles Soludo, bai taba yin zaben kananun hukumomi ba, sai yanzu da Kotun koli ta zartar da hukuncin bawa kananun hukumomi yancin cin gashin kansu da kuma hana nada shugabannin rikon kwarya.

Charles Soludo, ya sanar da cewa jam’iyyun siyasa 8 ne zasu shiga zaben, yayin da kwamishinan yada labaran Anambra Tony Nnalue, yace bashi da masaniya akan yawan jam’iyyun da suka shiga zaben.

Soludo, ya ce jam’iyyun da suka shiga zaben sun hadar da APGA, AA, LP, NNPP, PDP, da SDP.

Sanarwar lokacin gudanar da zaben ta yau 28 ga watan Satumba, ya haifar da cece-kuce tsakanin jam’iyyun hamayya inda suka ce an basu kurarren lokacin shiryawa shiga zaben.

Sai dai jam’iyyun APC da LP, sun kalubalanci salon yadda aka shirya zaben tare da alkawarin daukar matakin shari’a.

Sun ce babu kamshin gaskiya akan yadda gwamnatin jihar Anambra, ta shirya gudanar da zaben kananun hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here