Yahaya Bello ya shigar da EFCC kara gaban kotun Koli

0
46
Yahaya Bello

Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya shigar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC kara gaban kotun Koli.

Bello, ya shigar da karar ce yana kalubalantar EFCC saboda ta ayyana shi a matsayin wanda take neman kamawa ido rufe.

Yahaya Bello, yana fuskantar tuhume tuhume 19-da suka kunshi cin hanci da almundahana, bayan an zarge shi da halasta kudaden haram da yawan su yakai naira miliyan dubu 80 da dari 2.

Karanta karin wasu labaran:Jami’an hukumar EFCC sun karbi cin hanci da rashawa

Kafin yanzu an shigar da bukatar gabatar da shi tare da gurfana a gaban babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja a yau laraba.

Jagoran tawagar lauyoyin dake kare Yahaya Bello, A.M. Adoyi Emeka, ne ya shigar da karar neman a janye umarnin kama shi wanda aka bayar da umarnin tun ranar 17 ga watan Afrilu na Wannan shekara.

Haka zalika ya roki a jingine batun gurfanar da wanda yake karewa har sai an kammala shari’ar dake gaban babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja.

Yahaya Bello, ya daukaka karar ce mai lamba SC/CR/847/2024 da mai lamba SC/CR/848/2024.

Sai dai lauyan hukumar EFCC Kemi Pinheiro, mai lambar kwarewa ta SAN, ya nemi kotu ta bayar da damar ladabtar da mai kare Yahaya Bello don a saka masa takunkumi, bisa zargin sa da taimakawa Yahaya wajen raina darajar shari’a.

A baya dai kotun tace ba zata kuma cewa komai akan shari’ar ba har sai tsohon gwamnan jihar ta Kogi ya gurfana a gaban ta.

Idan za’a iya tunawa a watannin da suka gabata EFCC tayi kokarin kama Yahaya Bello, a gidan sa, hakan bai yiwu ba, wanda har sai da aka fuskanci harbe harbe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here