Jami’an hukumar EFCC sun karbi cin hanci da rashawa

0
72

Shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin ayi gaggawar fara binciken zargin da ake yiwa wasu jami’an hukumar na karbar cin hancin miliyoyin kudi.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, yana cewa jami’an hukumar EFCC sun karbi cin hanci na naira miliyan 15 daga wajen sa.

Kuranta wasu karin labaran: Badakala: EFCC ta damke tsohon ministan Buhari

Idan za’a iya tunawa a watannin baya hukumar EFCC ta kama tare da tsare Bobrisky akan wasu dalilai na zargin almundahanar kudade.

Okuneye, yayi zargin cewa jami’an sun karbi cin hanci daga wajen sa don a shafe zargin da ake yi masa na almundahanar kudade.

Bayan fitar Wannan zargi tuni shugaban ta EFCC ta kafa wata tawagar jami’an da zasu gudanar da bincike akan hakan don samo asalin gaskiyar abin daya kasance.

Akan hakan hukumar EFCC ta gayyaci Okuneye da Kuma Otse wanda shine ya fitar da faifan bidiyon zargin zuwa ofishin hukumar dake Legas don su taimakawa EFCC wajen gano gaskiya.

Mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale, ya tabbatarwa da yan Nigeria cewa zasu yi kwakkwaran bincike akan zargin da ake yiwa ma’aikatan nasu kuma zasu sanar da Sakamakon abin da suka samu ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here