Ɗangote ya bayyana dalilinsa na son a cire tallafin man fetur

0
69
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Alhaji Aliko Dangote ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta daina biyan tallafin man fetur.

A cewarsa tallafin mai zai janyo kashe kuɗaɗen gwamnati da bai kamata ba.

Ɗangote wanda ya bayyana hakan a wata hira da mujallar Bloomberg ranar Litinin.

Ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man ba.

Ku Karanta: Dillalan man fetur sun daina siyan mai daga matatar Dangote

“Ina ga lokaci ya yi da Najeriya za ta janye tallafin mai baki ɗaya domin dukkannin ƙasashe sun daina biyan shi.

Farashin manmu (Najeriya) kusan kaso 60 na farashjin mai a maƙwabtan ƙasashe kuma iyakokinmu na da girma saboda haka ci gaba da biyan zai yi wuya. Gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba.”

Dangote ya ƙara da cewa man fetur ɗin da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen farfaɗo da darajar naira.

“Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su riƙa ƙara yawan abun domin su samu ƙarin kuɗaɗe sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya.” In ji Ɗangote.

Dangane da yadda matatarsa za ta taimaka, Ɗangote ya ce:

“Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya faɗa maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi. Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. Amma mu yanzu za mu iya ƙididdigewa. Sannan za mu saka na’urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man.”

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here