NNPP ta sanar da mutanen da zasu yi mata takara a zabukan kananun hukumonin Kano

0
117

Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta fitar da jerin mutanen da zasu yi mata takara a zabukan kananun hukumoni dake tafe a wata mai kamawa.

An fitar da jerin sunayen mutanen a yammacin jiya Talata, wanda ake ganin hakan zai zama hanyar cigaba da fuskantar zaben ga magoya bayan NNPP har ma da yan takarar da suka samu Wannan dama.

Ku Karanta: Mahamat Idriss Deby  ya lashe zaben kasar Chadi

An dai tsayar da ranar 26 ga watan October a matsayin ranar gudanar da zaben.

Kafin yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta sanya naira miliyan 10 akan duk wanda yake neman takarar kujerar shugaban karamar hukuma, sai naira miliyan 5 akan duk wanda yake son zama Kansila, amma wata kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta dakatar da biyan kudin bayan da jam’iyyun APP da ADP suka kai kara akan hakan.

Ga jerin sunayen mutanen da suka samu takarar a jam’iyyar NNPP kamar haka,,,,,,,

Karamar hukumar Birni – Hon Saleem Hashim
Ajingi – Dr Abdulhadi Chula
Albasu – Garba hungu
Garko – Saminu Abdu
Dala – Surajo imam
Bichi – Hamza bichi
Gaya – Hon Muhammad Tajo
Nasarawa – Ogan Boye
Kumbotso – Ali Musa Hard Worker
Kunchi – Hashimu Garba Mai Sabulu
Bunkure – AB Muhammad
Gezawa mukaddas Bala jogana
Kura – Rabiu Sulaiman babina
Gwale – Hon mojo
Bebeji – Dr Alasan Ali
Fagge – Salisu Musa
Kabo – Hon Lawan Najume
Minjibir – Jibrin Nalado Aliyu
Tarauni – Ahmad Sekure
Makoda – Auwalu Currency
Sumaila – Farouq Abdu
R/Gado – Muhd Sani Salisu
Karaye – Hon Dan Haru
Rano – Naziru Ya’u
Bagwai – Bello Gadanya
Albasu – Garba Hungu
D/kudu – Sani Ahmad
D/Tofa – Anas Muktar Bello
Doguwa – Abdurrashid lurwan
Gabasawa – Sagir Musa
Gwarzo Dr Mani Tsoho
Kiru – Abdullahi Sa’idu
Rogo – Abba Na Ummaru
Wudil – Abba Muhammad Tukur
Tudun Wanda – Sa’adatu Salisu
Dambatta – Jamilu Abubakar
Shanano – Hon Habu Barau
Ungogo – Tijjani Amiru Rangaza.

Zamu kawo muku ragowar Kananan Hukumomin da basu sanar ba nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here