Dole a kawo karshen rashin tsaro a arewacin Nigeria–ACF

0
120

Biyo bayan gudanar da manyan taruka da kungiyar tuntuba ta Arewa ACF tayi da fitattun mutanen yankin da suka hadar da tsaffin Gwamnonin, ministocin, yan majalisar wakilai, da manyan malamai kungiyar ACF tace dole ne a kawo karshen rashin tsaron da yankin ke fuskanta.

Sakataren yada labaran ACF farfesa Tukur Muhammad Baba, ne ya karanto takardar bayan taron da suka gudanar, sun kuma kalubalanci salon da ake amfani da shi wajen yakar ayyukan ta’addanci da yan fashin daji a Arewa.

Ku Karanta: DSS ta rufe asibiti kan zargin rashin kwarewa a Jos

Tun da farko shugaban kwamitin amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewa Bashir Muhammad Dalhatu, ya nemi afuwar al’ummar Arewa akan yadda jagororin yankin suka gaza yin abunda ya dace daga abunda ake fuskanta na rashin tsaro da sauran matsaloli.

Dalhatu, yace suna yin kokarin kawo hanyoyin magance kalubalen da ake ciki a arewa da ma kasa baki daya.

An shirya taron da manufar mayar da martani akan sabbin matsalolin da ake ciki na karuwar ayyukan ta’addanci da tsadar rayuwa, rashin aikin yi, da sauran su.

An fitar da matsayar cewa dole ne yan arewa su hada kansu da yin aiki tare babu nuna ko wane irin kabilanci don kawo wa yankin mafita.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau, da Sanata Tanko Al-makura, sai tsohon Gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Adamu, da Janar Halilu Hakilu, Sanata Kabir Ibrahim Gaya, Sule Lamido, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here