Gwamnatin tarayya zata karawa yan Najeriya haraji

0
134
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar kara harajin siyan kayayyaki wanda aka fi sani da VAT daga kaso 7 da rabi cikin dari zuwa kaso 10 cikin dari.

Shugaban kwamitin da shugaban Kasa Tinubu ya samar akan harkokin kudi da farfado da fannin haraji Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan.

Taiwo, yace zasu mikawa majalisun dokokin kasa bukatar neman amincewa a kara harajin.

Ku Karanta: Yan sanda sun fara neman masu kokarin kifar da Gwamnatin Tinubu

Oyedele, ya sanar da hakan a yau lokacin da ake zantawa dashi a kafar talbijin ta Channels.

Amman yace kwamitin da yake jagoranta yana kokarin hade mabanbantan harajin da yan kasar nan ke biya zuwa waje guda da manufar rage yawan harajin da yan Nigeria ke biyan gwamnati.

A cewar shugaban kwamitin harajin yace nan bada jimawa zasu mika jadawalin shawarar da suka bayar akan harkokin karbar harajin ga majalisun kasa.

Oyedele, yace akwai kuskure a fannin haraji na Nigeria musamman akan tantance abubuwan da za’a karbi haraji akan su da wadanda ba sa bukatar a karbi haraji akan su.

Sai dai yiyuwar karin harajin ka iya kawo koma bayan tattalin arziki ga masu karamin karfi, Sakamakon yanayin karayar tattalin arziki da ake ciki, wanda haka yasa da yawa daga al’umma basa iya biyan bukatun su na yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here