Dillalan man fetur sun daina siyan mai daga matatar Dangote

0
90
Man Fetur
Man Fetur

Sabuwar matatar man fetur ta Dangote ta tabbatar da fara tace man fetur, a matatar dake jihar Legas.

Mataimakin shugaban sashin mai da iskar Gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ne ya sanar da hakan a jiya lokacin da ake zantawa da shi a shirin Brekete, wanda yace sun fara tace man fetur a ranar lahadi data gabata.

A cewar sa, ko kamfanin mai na NNPCL da sauran dillalan man fetur na kasar nan sun cigaba da kin siyan man daga matatar Dangote, to zasu fitar da abinda suke tacewa zuwa kasashen waje.

Ku Karanta: Benin ta hana Nijar fitar da fetur saboda rikicin kan iyaka

A yanzu dai ana tsaka da fuskantar karancin man fetur a fadin kasar nan, a daidai lokacin da gidajen mai mallakin NNPCL suke a kulle, sannan masu ababen hawa suna fuskantar hauhawar farashin mai da a yanzu kowacce lita daya ta zarce naira 1000, a gidajen man yan kasuwa.

Edward, yace dillalan man fetur a fadin kasar nan sun dena siyan man Diesel da man jirgin sama daga matatar Dangote tare da siyowa daga kasashen waje.

Matatar Dangote tace tun a baya tana tace man jirgin sama, da kalanzir, a daidai lokacin da suka fara tace man fetur a makon daya wuce, bayan haka Edward yace suna siyar da man jirgi da Kalanzir ga kasashen ketare saboda ba’a siya a Nigeria.

Matatar man tace fara tace man fetur da tayi abin farin ciki ne ga yan Nigeria a daidai lokacin da ake fuskantar karancin man.

Mataimakin shugaban sashin mai da iskar Gas na kamfanin Dangote Devakumar Edwin, yace suna fuskantar kalubalen hana su siyar da mai a kasar nan.

Idan za’a iya tunawa an samu dambarwa tsakanin matatar man fetur ta Dangote da kamfanin mai na NNPCL musamman akan kin siyarwa matatar danyen man da zata tace, wanda sai da hakan yasa shugaban kasa Tinubu ya shiga tsakanin su don samar da sasanci.

Masana tattalin arziki sun tabbatar da cewa idan aka kyale matatar man fetur ta Dangote tana samar da mai da iskar Gas a Kasar nan hakan zai inganta samar da ayyukan yi da saukin man fetur, sakamakon cewa daukacin man da ake amfani dashi a kasar nan ana shigowa dashi ne daga kasashen Turai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here