An yi jana’izar mahaifiyar Umar Musa Yar’adua

0
92
Mother of Late President Umaru Yar'adua, Hajiya Dada, Passes Away at 102 in Katsina
Mother of Late President Umaru Yar'adua, Hajiya Dada, Passes Away at 102 in Katsina

An gudanar da jana’izar mahaifiyar tsohon shugaban kasa marigayi Umar Musa Yar’adua Hajiya Dada Yar’adua, wadda ta rasu a yammacin litinin.

Hajiya Dada Yar’adua, ta rasu a asibitin koyarwa na Katsina, bayan fama da jinya.

An gabatar da jana’izar a babban filin kwallon kafa na jihar Katsina.

Ku Karanta: Hukumar hana cin hanci ta kama sakataren ilimi da shugaban firamare a Kano

Ta rasu tana da shekaru dari a duniya.

Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, da gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda, da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi.

Sauaran manyan mutanen da suka halarci jana’izar sun hadar da Sanata Ahmad Lawan, da Datti Baba Ahmad, sai Aminu Waziri Tambuwal, da Sanata Adamu Aliero, da Dahiru Mangal, sai kuma sarakunan jihar Katsina.

Fatan Allah ya gafarta mata, idan tamu tazo yasa mu cika da Imani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here