Ambaliyar ruwan saman zata haifar da karin tsadar kayan abinci

0
88
Rains-pains-Inside-Nigerias-recurring-flood-menace--1140x570
Rains-pains-Inside-Nigerias-recurring-flood-menace--1140x570

Wani binciken da Cibiyar kula da ayyukan gaggawa ta kasa (NEOC) tayi ya nuna cewa akwai yiwuwar fuskantar karin tsadar kayan abinci a Kasar nan, sakamakon yadda ambaliyar ruwan sama ta lalata amfanin gonaki da dama.

Cibiyar NEOC tace kawo yanzu ambaliyar ta shafi dubban kadada a gonakin dake fadin kasar nan.

Jihar Bauchi itace tafi kowacce jiha fuskantar kalubalen ambaliyar bisa hujjar da aka samu ta lalacewar gonaki 50, masu girman kadada 343, sai Taraba mai gonaki 22 kadada 182.

Ku Karanta: Gwamnatin Zamfara tayi alkawarin chanzawa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa

Haka zalika jihar jigawa ma ta fuskanci ambaliyar ruwan inda gonaki 9 masu girman kadada da 919 suka lalalace.

A Jihar Niger kuwa kadada 488 ce ta samu matsala, sai jihar Sokoto da kadada 676 ta lalace.

Sauaran jihohin da aka samu lalacewar gonakin sun hadar da Adamawa, Bayelsa, Borno, Ebonyi, Enugu, Kaduna, Gombe, Kano, Katsina, Kebbi, Yobe, da Zamfara.

Rahoton Cibiyar kula da ayyukan gaggawar na Wannan shekara yace jihohi 29, ne suka samu ambaliyar, a cikin kananun hukumoni 154, haka ne yasa dubban mutane suka rasa muhallin su, da da asarar rayuka.

Yawaitar ambaliyar ruwan saman ya kawo koma bayan samun abincin da ake bukata, Kuma yayi sanadiyyar samun hauhawar farashin kayan masarufi da kaso 40 cikin dari.

Ko a jiya litinin sai da bankin kasa CBN yace yanayin hauhawar farashin kayan masarufi zai sa al’ummar kasar nan su kashe kudade masu yawa a fannin siyan abinci nan da watanni 6 masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here