Yan sanda sun fara neman masu kokarin kifar da Gwamnatin Tinubu

0
154

Rundunar yan sanda ta kasa ta bayyana wasu mutane biyu a matsayin wadanda take nema ido rufe.

Mutanen sun hadar wani dan asalin kasar Burtaniya mai suna Andrew Wyenne da kuma dan kasar nan mai suna Lucky Obiyan.

Rundunar yan sandan tace tana zargin mutanen da kokarin kitsa yadda za’a kifar da Gwamnatin shugaba Tinubu.

Ku Karanta: Tinubu zai kori wasu daga cikin ministocin sa

Yan sandan sunce akwai zargin Andrew, ya shirya makarkashiyar rusha Gwamnatin tarayyar kasar nan ta hanyar kawo hargitsi a Nigeria.

Kakakin rundunar yan sanda na kasa Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake yin jawabin sa ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Yace rundunar yan sanda ta gudanar da binciken kwakwaf akan al’amuran cikin gida da ketare don binciko yunkurin da wasu keyi na rushe zababbiyar Gwamnatin kasar nan.

Zuwa yanzu an kama mutane 9, wadanda aka tabbatar da sun karbi kudaden da zasu yi aikin kawo hargitsi a Nigeria, Kuma an gane cewa sun karbo kudaden ne daga wasu yan kasashen waje, inji rundunar yan sandan.

A cewar rundunar yan sandan anyi amfani da kudaden wajen daukar nauyin masu zanga zangar da aka gudanar a kasar nan a watan Ogustan daya gabata, da kuma yada kalaman da bana gaskiya ba.

Cikakkun hujjoji sun bayyana cewa Wyenne dan kasar Burtaniya ya bayar da kudade da wasu dabarun da za’a yi amfani da su don kifar da gwamnatin Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here